Kungiyar ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki

Alfijr

Alfijr ta rawaito, a karshe dai bayan kammala zaman kwanaki biyu tsakanin masu ruwa da tsaki a Kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU a yau Litinin ta kungiyar ta sanar da tsunduma yajin aiki na gargadi na tsawon sati 4

Alfijr

Sanarwar ta a wani taron manema labarai da ya gudana a safiyar yau kungiyar tace zata yi yajin aiki na sati 4 a sassan kasar nan, Kamar yadda Shugaban kungiyar na kasa farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana.