Buhari Ya Zabi Wanda Zai Zama Shugaban Najeriya Na gaba

Alfijr

Alfijr ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda aka ba wa takardar kudirin barin mulki nan da watanni 15, ya shirya jerin sunayen mutane guda uku, inda a karshe za a zabi daya a matsayin wanda zai gaje shi, kuma hakan ya tabbata.

Alfijr

Wata majiya ta bayyana wa Mujallar OpenLife a safiyar Juma’a ta ce an dauki matakin ne a ziyararsa ta karshe zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha, domin halartar taron shugabannin kasashen Afirka karo na 35.

Taron na Habasha ya kasance wata dama ce da ake bukata ga Buhari ya tara ’yan kwamitinsa na ciki wanda a cewar majiyar, ya tashi zuwa Addis Ababa don kawar da duk wani shubuhar da ka iya tasowa daga makusantansa.

Alfijr

Majiyar ta kara da cewa an samu wakilcin bukatun kasashen waje da kuma gabatar da su “Saboda amincewar kasashen duniya na zabin Buhari na da matukar muhimmanci”, in ji shi.

Majiyar ta kara da cewa, a karshe an zabo tsohon shugaban kasa Ebele Jonathan, Adams Oshiomhole da Ogbonnaya Onu, ministan kimiyya da fasaha na yanzu sannan aka ce Baba ya ajiye korafin siyasa a gefe ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da kuma Abdulsalam Abubakar da samun amincewarsu in ji shi.

Alfijr

Sai dai majiyar ta kara da cewa Buhari ya amince ya gana da takwarorinsa na soja amma “Obasanjo na iya zama mai wuyar sha ani kuma karbuwarsa na da matukar muhimmanci sosai.

Slide Up
x