Alfijr
Alfijr ta rawaito, kamfanin dillancin labaran na kasar Malaysia ya tabbatar da cewa, wani jirgin fasinja na kamfanin AirAsia, yayi saukar dole ba tare da an shirya shi ba, bayan da aka hangi maciji ya lallaba ta cikin fitilun da ke sama a cikin jirgin.
Alfijr
Lamarin, wanda kamfanin jirgin ya bayyana, ya faru ne a makon da ya gabata a cikin wani jirgin da ya taso daga Kuala Lumpur babban birnin kasar zuwa Tawau, a gabar tekun gabashin tsibirin Borneo.
Bayan da kyaftin din ya samu labarin maciji, sai ya dauki “matakin da ya dace” ya sauka a birnin Kuching mai tazarar kilomita 900 daga yammacin Tawau, don haka za a iya tursasa jirgin, in ji AirAsia.
Alfijr
Daga nan fasinjojin suka sake hawa wani jirgin domin ci gaba da tafiya.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in tsaron AirAsia, Liong Tien Ling ya fitar, ya ce “Babu wani lokaci da lafiyar baƙi ko ma’aikatan jirgin suka kasance cikin barazanar haɗari sai wannan Karon.”
Alfijr
Wani hasashe da jama a suka yi sun ce, lamarin ya kasance kamar wani fim da aka yi 2006 wanda ya nuna Jackson a matsayin jami’in FBI da ya makale a cikin jirgi mai cike da macizai.