Jami an Kwastam Sun kama Wasu Manyan Motoci, Na ₦529m Da Tramadol Na ₦192m Da Sauran Kayayyaki

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar Kwastam ta kama wasu manyan Motoci, wasu da kudinsu ya kai N529m Ya kuma ce, katan 640 na magunguna marasa rajista da suka hada da tramadol da kudinsu ya kai Naira miliyan 192, dauke da babbar mota kirar DAF da wata motar bas ta J5 ta hanyar Okada/Benin.

Shugaban hukumar Kwastam Kanal Hameed Ali ya kara da cewa, an kama bale 1,650 na rigunan da aka yi amfani da su, wanda darajarsu ta kai Naira miliyan 165 a kan hanyar Umuikaa/Aba, yayin da buhunan shinkafa 181 50kg na kasar waje da ta kai sama da Naira miliyan 7.2 aka kama ta hanyar Akwa-Ibom/Calabar.

Haka kuma an kama guda 2,239 na tayoyin da aka yi amfani da su a kan naira miliyan 4.5 da lita 36,000 na man da aka yi fasakwaurinsu a cikin buhunan polyethylene, wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 3.6.

Alfijr

Ibrahim ya godewa Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali (Rtd) da tawagarsa bisa goyon baya da kwarin gwiwa da suka ba shi, yayin da ya jajanta wa iyalai da ‘yan uwa na jami’ai hudu da suka rasu suna bakin aiki.

A cewarsa, hukumar na hada kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da ci gaba da tsaron jami’anta da mutanen.