Matasa Ku Shiga Siyasar Jam’iyya, a Dama Da ku! Inji Comrade Maihula

Alfijir

Alfijir

Alfijir ta rawaito wani matashi Muhd Dahiru Mai Hula yayi kira ga matasa da su shiga duk wani abu da zai daukaka da bunkasa rayuwarsu tare da kawo habakar tattalin arzuki a Nigeria.

Maihula wani dan Jarida ne a Kano, in da ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a taron matasa da aka gudanar a garin Kano.

Alfijir

Dahiru Maihula ya ce lokaci ya yi da ya kamata a matasa su tsunduma cikin harkokin siyasar jam’iyya, da kuma tsarin zabe mai zuwa a shekarar 2023 don kawo karshen danniya da ake yi wa matasa a kasar

Zaku iya tuna cewa dokar ta ‘Not too young to takasa’ ta kasance doka ne a kasar, don ba da dama ga matasa su shiga cikin tsarin domin a dama da su a fadin kasar.

Slide Up
x