Na daina jin Tausayin Ƴan Najeriya domin Su Suka Janyowa Kansu- In Ji Sule Lamido

FB IMG 1739902716758

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Suke Lamido A Hirar da akayi dashi A BBC Hausa ya bayyana cewa yan Najeriya sune suka jefa kansu cikin halin da suke ciki,

Lamido Ya bada misali da cewa masu kada kuri’a ba mahaukata bane, kasan APC kasan PDP kuma kasan yan takarar su, hakazalika kasan wanda Ya dace kasan wanda bai dace ba, sannan da hannun ka zaka jefa kuri’a a ranar zaɓe, saboda haka Ni a nawa tunanin yan Najeriya sune suka jefa kansu Cikin Halin da suke ciki a yanzu.

Sule Lamido Ya Kara da cewa, batun korafe-korafe da yan Najeriya suke ba mafita bane, su cigaba da Addu’ar Allah ya basu ikon gyara kuskuren da suka yi na zaɓar jam’iyyar da bata dace dasu ba

Daga ƙarshe Ɗan jaridar Ya  Tambaye Sule Lamido Cewar Tinubu ya taɓa tuntuɓar sa Domin Bashi shawarwari domin A daƙile Wahalhalun da al’ummar Najeriya suke fama dashi, ya bayyana cewa ba’a name shi ba, kuma yasan ba za’a yi hakan ba! Domin ba’a ɗauki layin aiwatar da hakan ba tukunna.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *