Alfijr
Alfijr ta rawaito, rundunar ‘Yan-Sandan Najeriya reshenjihar Jigawa ta kama wani magidanci da ake zargin ya kashe ‘yarsa ta hanyar duka
Alfijr
Magidancin mai suna Hannafi Yakubu mai mazaunin ‘kauyan Aciya dake ‘karamar hukumar ‘Babura, ana zargin ya daki ‘yar tasa mai suna Salima Hannafi mai shekaru 11 ne, wadda ya yi sanadiyyar rasuwarta.
Kakakin Rundunar ‘Yan-Sandan jihar Jigawa ASP Lawan Shisu Adam yace an tabbatar da mutuwar yarinyar ne bayan kaita Asibiti
Alfijr
Kazalika yace tini suka gara gudanar da bincike domin gurfanar da mutumin gaban ‘kuliya manta sabo don girbar abinda ya shuka.