Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wasu ‘Yan Kasashen Waje Ɗauke Da Kokon Kan Mutane Da Kasusuwa


Alfijr ta rawaito wasu ‘yan kasashen waje guda biyu da ‘yan sanda suka kama da kokon kan mutane, da kasusuwa biyu da ake zargi da suna Nodji Kodji da Raji Silver

Alfijr Labarai

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu ‘yan kasashen waje da kokon kan mutane da kasusuwa da dama a kauyen Garware da ke karamar hukumar Fufore, karamar Hukumar Mulki.

Rundunar ta kuma kama wani da ake zargin shi yake siya mai suna Dauda Yakubu ɗan Achaba ne, da wata mata da ake zargi da aikata laifin.

An kama su Nodji da Raji ne a ranar 11 ga Oktoba, 2022, kuma sun fito ne daga Cholli, al’ummar Jamhuriyar Kamaru a kauyen Garware.

Alfijr Labarai

Wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa sun samu kokon kai da kasusuwan ne daga wata makabarta a kasar Kamaru inda suka so sayar wa Dauda kan kudi CFA miliyan 5.

Sun bayyana cewa a lokacin da suka kai kokon kan wurin Dauda ya ce ba shi da sha’awa kuma a lokacin da suke neman wani mai saye shine aka kama su.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Sulaiman Yahaya Nguroje, ya ce jami’an ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargin wadanda ke sintiri na yau da kullum a yankin.

A lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin, Nguroje ya bayyana cewa, tawagar karkashin jagorancin CSP Usman Jauroyel ne suka kama wadanda ake zargin.

Alfijr Labarai

Ya kara da cewa wannan wata gagarumar nasara ce da rundunar ta samu a kokarinta na yaki da duk wani laifi.

Kakakin ya ce dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin satar kokon kai da kasusuwa a makabarta a wani kauye a Jamhuriyar Kamaru tare da kawo su Najeriya don sayarwa.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, A.K Akande ya bayar da umarnin a mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike mai inganci.

Sulaiman ya ba da shawarar cewa ya kamata a samar da isasshen tsaro a makabarta don hana faruwar hakan.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *