
Alfijr ta rawaito a kalla mutane 20 ne suka samu raunuka daban-daban lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC da babbar abokiyar hamayyarta PDP suka fafata a unguwa ta 7 a Karamar Hukumar Ibarapa Gabas ta Gabas ta Jihar Oyo.
Wannan lamari ya faru ne da sanyin safiyar yau Asabar, 18 ga watan Maris, 2023, yayin da ake shirin fara zaben gwamna.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne lokacin da wasu da ake zargin magoya bayan jam’iyyar PDP ne suka kai hari kan wata motar bas dauke da wasu mutane zuwa filin zabe a wani harin ramuwar gayya.

Wata majiya ta bayyana cewar wasu magoya bayan jam’iyyar APC sun gano jagororin maharan zuwa maboyar su inda ‘yan ta’addan suka kai hari. -duk ya biyo bayan raunata mutane da dama.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ