Sanata Natasha ta maka shugaban majalisar dattijo Akpabio a kotu kan zargin ɓata suna

FB IMG 1740576450455

Daga A’isha Salisu Ishaq

Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar dattajai, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna.

Natsha ta shigar da karar ne gaban babbar kotun tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick.

Ta nemi kotun tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara.

Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya bayyana cewar kalaman da babban mai taimaka wa shugaban majalisar dattawan Najeriyar ya wallafa a shafinsa na facebook.

Barista Giwa ya yi zargin cewar kalaman ba komai ba ne illa, ɓata suna, da tsokanar fada, da ƙanskantar da ita a idon abokan aikinta, da sauran al’umma.

Sanata Natasha ta bukaci kotun da ta haramta wa waɗanda ake ƙara ko makusantansa daga wallafa duk wani rubutu na batanci a game da ita.

A makon da ya gabata ne Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwarta kan yadda aka bai wa wani dan majalisa wurin zamanta, saboda wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman majalisar. Inda ta ki amincewa da sauyin wajen zaman da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ta da shugaban majalisar dattawan.

Tuni aka umarci kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawan da ya gayyaci Sanata Natasha don bin bahasi kan rikicin sauyin wajen zaman.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *