Alfijr ta rawaito sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce tun farko aka sanya ta a karkashin kulawar likita ta mutu.
Alfijr Labarai
Da yake sanar da rasuwarta, Fadar Buckingham ta fitar da wata sanarwa cewar, “Sarauniya ta mutu cikin lumana a Balmoral da yammacin yau.
Sarki da Sarauniya Consort za su kasance a Balmoral a yammacin yau kuma za su koma Landan gobe.
Mutuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu ta zowa mutanen Biritaniya, a lokaci guda ba ta da misaltuwa kuma Colin bazata.
Alfijr Labarai
Sarauniyar Ta rasu tana da shekaru 96 a duniya, bayan fama da rashin lafiya da ta Shaktar fama
Mijin Sarauniyar, Yarima Philip, ya riga ta rasuwa, wanda ya rasu a ranar 9 ga Afrilu, 2021, yana da shekaru 99 a duniya.
Sarauniya Elizabeth ta bar ‘ya’yanta maza uku, Yarima Charles, Andrew da Edward; da kuma mace, Gimbiya Anne; jikoki takwas, Yarima William da Harry na Wales, Gimbiya Beatrice da Eugenie na York, da Peter da Zara Phillips, da kuma Lady Louise Windsor da James, Viscount Severn. Ta kuma rasu ta bar jikoki 12.