Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bayyana cewa yau Litinin, 25 ga Agusta 2025, ita ce 1 ga watan Rabi’ul Awwal 1447 bayan hijira.
Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, ba a samu ganin jinjirin watan Rabi’ul Awwal ba a ranar Asabar, lamarin da ya tabbatar cewa Lahadi ce ta cika kwanaki 30 na watan Safar.
Saboda haka, Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin a matsayin farkon watan Rabi’ul Awwal, bisa amincewa da rahotannin hukumomin da ke da alhakin ganin jinjirin wata a sassa daban-daban na ƙasar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t