Alfijr
Alfijr ta rawaito wata babbar kotun jihar Kano mai lamba 15, karkashin jagorancin Mai Shari’a Jamilu Shehu Sulaiman ta fara sauraron shaida bisa tuhumar da hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta ke yiwa shugaban karamar hukumar Fagge.
Ana shugaban karamar hukumar Fagge Hon Ibrahim Muhammad Shehi ne da laifin bayar da cin hanci ga wasu ma,aikatan tattara haraji a matsayin kasonsu, maimakon a basu kaso 2 zuwa 5 kamar yanda dokar ta tanada sai ake basu kaso 20, cikin zarhin da kukumar ICPC ta yi masa
A nasa bangaren dai Shehi ya musanta zargin da ake masa.
Alfijr
A zaman kotun na ranar Litinin, lauyoyin hukumar sun gabatar da shaida na farko sun kuma dauki alkawarin kawo ragowar shaidunsu a zaman na yau Litinin 7th/03/2022
Mai shari’a Jamilu Shehu Sulaiman ya sanya ranar 12 ga watan 5 dan cigaba da sauraron shaidun da lauyoyin hukumar zasu kawo.
Alfijr