Wata Kotu Ta Daure Yusuf Ibrahim Dake Unguwar Yalwa Shekaru 16 Bisa Laifin Luwadi A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito mai shari’a
Amina Adamu Aliyu dake kotu mai lamba 10 Miller Road a kano, ta daure wani mai suna Yusuf Ibrahim dake unguwar Yalwa karamar hukumar Dala ta jihar Kano shekaru 16 da tarar dubu 20,000

Alfijr

An gurfanar da Yusuf ne a gaban kotun bisa zargin yin Luwadi da yara biyu, daya mai shekaru 3 dayan kuma mai shekara sha 13.

Yusuf dai ya lalata yaro na farko ne mai shekara 3 a gidansu inda suke kwana tare dashi, a ranar 13 Agusta 2015, sannan ya lalata yaro na biyu kuma 13 Octoba 2015, kamar yadda masu bincike suka tabbatar.

Alfijr

Lauyoyin gwamnati sun tabbatar da shaidun faruwar haka bisa kawo shaidu har 3.

Wanda ake zargin a zaman na yau ya kara tabbatarwa da kotu ya aikata laifin da ake zarginsa dashi bisa damar da aka bashi ta kariya.

Kotu ta kara tambayar lauyan gwamnati an taba kamashi da irin wannan laifin, lauya yace bai sani ba.

Alfijr

Shi kuwa lauya mai kare shi ya roki kotu da ta yi masa sassauci bisa amsa laifinsa babu wahalar da kotu.

Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu da take yanke masa hukunci ta daure shi shekaru 8 a laifin farko 8, a laifi na biyu, amma hukuncin zai tafi bai daya 8 cikin 8,

Alfijr

Sannan sai tarar kudi dubu 20,000, kuma ɗaurin za a fara lissafine tun randa aka daure shi 2015.

Slide Up
x