Tirka-Tirka! ‘Sakin’ Murja Kunya Ya Bar Baya Da Kura A Kano

FB IMG 1708339212755

Al’umma a jihar Kano na ci gaba da ce-ce-ku-ce kan rahoton da ke nuna fitacciyar ƴar Tiktok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya – da a baya-bayan nan kotu ta tasa ƙeyarta zuwa gidan yari ta shaƙi iskar ƴanci.

Alfijir labarai ta rawaito a makon da ya gabata ne kotun shari’ar musuluncin da ke Gama ta bayar da umarnin a tsare Murja a gidan gyaran hali na Kurmawa bayan da Hukumar Hisbah ta kama ta bisa zargin nuna rashin ɗa’a da yunƙurin jefa ƴanmata cikin karuwanci.

Kotun dai ta nemi a tsare ƴar Tiktok ɗin ne har zuwa ranar Laraba 27 ga watan Fabarairu sai dai bayanai na cewa an bayar da belin ta, lamarin da ya fusata wasu al’ummar jihar.

Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun yi ta bayyana ra’ayinsu kan yadda ake cewa Murja Kunya ta samu beli duk da cewa kotu ta bukaci a tsare ta har ranar Laraba.

Kakakin kotun Musulunci, Muzammil Ado Ibrahim Fagge na cewa bai san da faruwar lamarin ba.

Ya ce “mun kuma ji cewa an sake ta daga gidan yari. Alƙalin kotun ya ce zai yanke shawara kan ko ya ba ta beli ko a a, a ranar 20 ga watan Fabarairu. “Ba mu san abin da ya faru ba. Ba za a iya sauya abin da ya faru a kotu ba musamman kan wannan yarinyar da ba wannan ne karon farko ba.”

A nashi ɓangaren, mai magana da yawun hukumar gidan gyaran halin, Musbahu Kofar Nassarawa ya ce an sake ta ne bayan samun umarni daga kotu.

Ya ce hukumar gidan gyaran halin na tafiya ne bisa tsarin doka kuma tana aiki ne kamar banki, “takardu ke shigar da kai, irin takardun kuma ke fitar da kai.”

“Dole ne alƙali ya sa hannu a tura ka gidan yari, haka nan idan za a sake ka.”Kan batun Murja, babu wanda ya tsere daga gidan yari. Idan ka hau katanga a ƙoƙarin tserewa, daidai yake da a ɗauki matakin harbe mutum kuma muna da ƙofofi da jami’ai ke tsaronsu.

Wani jami’i a hukumar hisbah da ke Kano wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ba zai shafi ayyukan jami’ansu ba saboda ba za su naɗe hannu ba a yaƙi da baɗala a jihar Kano.

Tuhumar da ake yi wa Murja:

A wata tattaunawa da manema labaru bayan kama ƴar tiktok ɗin, kwamandan Hizba a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al’umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al’umma, kawo ɓatagari cikin unguwa, iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *