Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles Da Kano Pillars Ya Rasu Yana Da Shekara 34. Hade Da Tarihinsa

Alfijr ta rawaito Tsohon dan wasan Super Eagles da Kano Pillars, Bello Musa Kofar Mata ya rasu.

Alfijr Labarai

Musa ya rasu ne da yammacin ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, 2022, a mahaifarsa ta Kano bayan gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin yana da shekaru 34, an gudanar da jana’izar marigayin a safiyar yau Laraba, 2 ga Nuwamba, 2022, a gidan iyalansa da ke Kofar Mata, Jihar Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kofar Mata ya fara wasan kwallon kafa ne a shekarar 2007 da kungiyar Buffalo F.C ta Kano, wanda a shekarar ne ya koma kungiyar Kano Pillars.

Alfijr Labarai

A shekarar 2010 ya koma kungiyar Heartland FC ta Owerri inda ya koma Kano Pillars a shekarar 2012, sannan ya wuce Elkanemi Warriors na Maiduguri.

Bello ya kulla yarjejeniya da IK Start ta kasar Norway, biyo bayan da kungiyar Kano Pillars, ya lashe gasar Premier ta Najeriya a 2007-08 kuma yana da kwallaye 11 da ya fi zura kwallaye.

A watan Agusta 2008, Kofar Mata yana kan gwaji a LASK na Austria kuma ya buga wasan sada zumunci guda daya.

Hakazalika Dan wasan ya dawo daga Turai zuwa Pillars a farkon kakar 2008.

Alfijr Labarai

Ya koma Heartland a watan Janairun 2010 akan kudi naira miliyan biyar.

Bayan shekara biyu da rabi ya bar Heartland ya kulla yarjejeniya da kungiyarsa ta Kano Pillars.

Marigayi Kofar Mata yana cikin tawagar Najeriya a gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 na 2007 a Canada.

Ya buga wasansa na farko na Super Eagles ne a watan Maris din shekarar 2010, inda ya maye gurbinsa a wasan sada zumunta da suka doke DR Congo da ci 5-2 a Abuja.

Alfijr Labarai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *