Wani Matashi Ya Sassara Babansa Da Babarsa, Kuma Sun Mutu Har Lahira


Alfijr ta rawaito wani matashi dan shekara 21, dalibi a Jami a ya kashe iyayensa bayan da ya nemi kudade a hannunsu suka hana shi ganin shine da ɗaya tilo a wajen su.

Alfijr Labarai

An tsinci gawar dattawan ne bayan sun fara rubewa, an same su ne duk jikinsu da saran adda kaca kaca a ranar Alhamis a garin Nnewi da ke Jihar Anambra.

An gano gawarwakin ne bayan wari ya addabi makwabta a unguwar Abubor Nnewichi-Nnewi ne, jama ar unguwar suka yi ta neman inda warin ke fitowa.

Makotan gidansu matashin sun tabbatar da cewa ya na ta’ammali da miyagun kwayoyi irin su Mkpurummiri da Methamphetamine.

Ana kuma zargin ya kashe iyayen nasa ne bayan wata takaddama, saboda sun hana shi kudin da ya bukata a gare su, kuma ya tsere tsawon kwanaki 3 babu labarinsa

Alfijr Labarai

DSP Ikenga Tochukwu, wanda shine kakakin rundunar ƴan Sandan jahar Anambra ya ce, saran adda da aka samu a jikin gawarwakin alama ce ta an aikata musu rashin imani.

Ya kara da cewa rundunar ta fara farautar wanda ake zargin lungu da sako na fadin jihar, kuma ya tabbatar da cewar kwamishinan ƴan Sandan jahar ya bada umarnin mai da laifin, zuwa babban sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin gudanar da zuzzurfan bincike.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *