An Gano Dan Gidan Dr Zahra’u Kwamishiniyar Mata Da Ya Bata A Kano.

Alfijr

Alfijr ta rawaito, bayan sama da makon 2 da bacewar dan gidan malama Dr Zahra’u wadda take a matsayin Kwamishiniyar mata a Kano, yanzu dai Allah ya bayyana Abdurrahman.

Alfijr

A tattaunawar jaridar Alfijr ta yi da Dr Zahra’u ta bayyana mana cewa yan sanda caji office dake kwanar dan Gora sune suka shaida mata ganin dan nata Abdurrahman

Yanzu haka Dr Zahra’u ta ce yaron na nan ana duba lafiyarsa.

Dr Zahara ta kara godiya ga Allah da kuma jama ar da suka taya ta da addu a har Allah ya bayyana musu yaron nasu.

Slide Up
x