Wasu Tarin ‘Yan Daba Sun Farwa Marasa Lafiya A Asibtin Murtala Kano

Alfijr ta rawaito wasu fusatattun yan daba sun kunna kai cikin Asibitin Kwararru na Murtala dake kwaryar birnin Kano.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe uku na daren ranar Alhamis, inda ‘yan dabar suka yiwa asibitin dirar mikiya cikin tsakar dare, wanda ake zaton sun haura sama da arba’in dauke da muggan makamai suka kuma afka bangaren bada taimakon gaggawa Wato Emagency.

Alfijr jiyo daga bakin wani ma aikaci asibitin cewar, yan dabar sun kwacewa masu jiyya wayoyinsu da jefe jefe a cikin asibitin da sauran kayayyaki da suka dinga kwacewa masu jinya, sun dauki dogon lokaci suna cin karensu babu babbaka a cikin asibitin.

Alfijr

Wasu ganau da abin ya faru akan idonsu, sun bayyana cewa hatta jami’an tsaro da suke wannan bangare suma guduwa sukai Sakamakon yadda lamarin ya fi karfinsu.

Mun yi kokarin jin ta bakin mahunkunta abin yaci tura, amma idan hali yayi Zaku ji cikakken bayani daga bisani.

Slide Up
x