Wata Gobara Ta Lakume Rayukan Mutane 8, Da Jikkata mutane Da Dama A Wani Katafaren Gini

Alfijr ta rawaito Akalla mutane takwas ne suka mutu wasu da dama kuma suka samu raunuka bayan wata gagarumar gobara ta tashi a wani dakin baje kolin lantarki a birnin Secunderabad na kasar Indiya da yammacin Litinin Litinin.

Alfijr Labarai

Wutar da ta tashi ta bazu har zuwa wani otal da ke saman bene mai hawa daya na gini, in da akalla baki 25 ke zama.

Secunderabad cibiyar masana’antu ce a kudancin jihar Telangana, wanda Hyderabad babban birni ne a kasar India.

Jami’ai sun ce gobarar ta tashi ne a dakin baje kolin lantarki da ke kasan ginin, kuma ba da dadewa ba ta bazu zuwa otal din Ruby Pride.

Sun kara da cewa dukkan mutanen takwas da alamun sun mutu ne saboda shakar hayakin.

Alfijr Labarai

Sanarwar ta ce, hayakin ya ratsa ta matakalar ne, tun daga kasa har zuwa saman bene, wasu mutanen da suke barci a hawa na daya da na biyu sun shaki hayakin ne suka mutu sakamakon shanyewar numfashi,” in ji CV Anand. kwamishinan ‘yan sanda na Hyderabad.

Hukumar kashe gobara ta kubutar da mutane da dama ta hanyar amfani da tsani na crane, yayin da wasu ‘yan yankin suma suka shiga tare da taimakawa wajen ayyukan ceto, in ji jami’ai.

Hotunan kuma sun nuna yadda wasu mutane ke tsalle daga tagogin otal din da nufin tserewa.

Alfijr Labarai

Anand ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban na birnin domin yi musu magani kuma an shawo kan gobarar.

Ya ce suna gudanar da bincike kan ko gobarar ta tashi ne saboda yawan cajin batura a dakin baje kolin lantarki ko kuma a cikin dakin ajiye motoci masu yawa na lantarki.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Chandana Deepti mataimakiyar kwamishina Hyderabad na cewa “bamu sani ba ko gobarar ta tashi ne saboda karin caji sannan kuma ta bazu ko kuma ta fara ne ta wani wurin.

Alfijr Labarai

Jami’ai sun ce tsarin yayyafa ruwa a ginin bai yi aiki ba a lokacin da gobarar ta tashi – wanda a yanzu ake bincike.

Ministan cikin gida na Telangana Mohammad Mehmood Ali ya jajantawa asarar rayuka sannan ya ce an bayar da umarnin gudanar da bincike don gano ainihin musabbabin tashin gobarar.

“Rundunar ‘yan kwana-kwana sun yi iya kokarinsu wajen ceto mutane daga masaukin amma saboda tsananin hayaki, wasu sun mutu, muna kan binciken yadda lamarin ya faru kuma an fara shirye shiryen bincikar lamarin.” Inji shi.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *