Alfijr ta rawaito, Khalifah Muhammad Sanusi II zai kasance babban bako na musamman mai jawabi a taron majalisar dinkin duniya na musamman akan ilimi da inganta koyarwa musamman a kasashe masu tasowa.
Alfijr Labarai
Khalifah Muhammad Sanusi II yana daga cikin mutanen da Majalisar dinkin duniya ta zaba domin su jagoranci hanyoyi daban daban na inganta rayuwar Jama’ah a kasashe daban daban na duniya.
Za’ayi wannan taro ranar Asabar mai zuwa 17 ga watan da muke ciki na Satumba, a babbar hedikwatar majalisar dinkin Duniya dake kasar Amurka.