Wata Gobarar Da Ta Tashi Tsakar Dare Ta Ƙone Gidaje Tare Da Wani Ɗan shekara 50

Alfijr ta rawaito wani ibtila’i ya faru a ranar Lahadi, yayin da wani mutum da har yanzu ba a kai ga gane ko wanene ba ya rasa ransa a wata gobara da ta tashi da tsakar dare a yankin Bariga da ke jihar Lagos.

Alfijr Labarai

Gobarar da ta faru da misalin karfe 3 na safe, ta kone ɗakuna 10 a cikin wani gida mai ɗakuna 25 da shaguna 18.

Daga bisani, wata gobara ta sake afkuwa a wani gida mai dakuna takwas da shaguna hudu a yankin Somolu na jihar.

Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Lagos, Margaret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi.

Ta ƙara da cewa, “Hukumar kashe gobara ta jihar Lagos cikin dare ta yi nasarar kashe gobara guda biyu a yankin Bariga da Somolu na jihar.

Alfijr Labarai

Sanar farko an sanar ne cikin gaggawa da misalin karfe 12:31 na safiyar Lahadi, zuwa 19, titin Apata, Somolu, yayin da aka sanar da ta biyun daga karfe 3.19 na safe zuwa 48, titin Jagunmolu, Bariga, a daidai lokacin da aka kammala aikin kashe gobara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

The PUNCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *