Wata Kotu Ta Aike Da Kansilan Garin Kura Hon Mai Gida Sani Gidan Gyaran Hali

Daga Rabiu Usman

Alfijr ta rawaito an gurfanar da wani dattijo mai Shekaru 58, gaga kotun majistare mai lamba 61 dake zaman ta a unguwar mariri cikin birnin kano, karkashin mai Shari’ah Salisu Idris Sallama

Alfijr Labarai

An gurfanar da Mai gida Sani wanda ke guda daga cikin kansilolin Karamar hukumar kura, bisa zargin sa da laifin Zagin Cin Mutunci, bata suna, fadar magana mai fusata Mutum, da Bayanan karya, harma da maganganu masu haifar da rashin zaman lafiya ga shugaban Karamar hukumar Kura Hon Mustapha Abdullahi.

Bayan da mai gabatar da kara a gaban kotun Barr Mahadi ya karanto kun shin tuhumar da ake yiwa mai gida sani, nan take ya musanta dukkannin laifukan da ake zargin sa dasu.

Hakan ne ta baiwa Mahadi damar sake daukar wata Rana domin sake gabatar da mai gida sani gaban wannan kotu, nan take kuma kotun ta sanya ranar 22nd ga watan da muke ciki domin dawowa kotun domin dorawa daga inda kotun ta taya.

Alfijr Labarai

Jim kadan da fitowa daga kotun wakilin alfijr ya ji ta bakin lauyan da yake kare mai gida sani, Barr Yusuf Mu’az Sani tare da abokin aikin sa Barr Muhammad Aliyu Tijjani, don neman karin bayani bisa wanda suke karewa.

Barr Yusuf yace babu abinda zaice akan wannan takaddama tsakanin Shugaban karamar Hukumar Kura Hon Mustapha Abdullahi tare da Kansila Mai gida sani.

Sai dai a karshe Kotu ta sanya me gida sani a hannun beli, mutane 2 zasu tsaya masa 1, limamin masallacin juma’a, 1, Mutum mai kamala, sannan zasu ajiye hotunan su guda 2, Dan sandan kotu zaije ya gano Gidajen su, za’a ajiye kudi a kotu naira dubu Dari biyu, a karshe kuma zasu cike takardar rantsuwa a babbar kotun jiha wadda take nuna kadarorin da suka mallaka.

Alfijr Labarai

Asc Musa yola Jami’in Gidan Ajiya da gyaran hali ya tisa keyar Hon Kansila mai gida sani zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya domin cika Ulumarnin kotu.

Slide Up
x

One Reply to “Wata Kotu Ta Aike Da Kansilan Garin Kura Hon Mai Gida Sani Gidan Gyaran Hali”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *