Bayan Ragargaje Yar Sanda Da Tayi, Kotu Ta Aike Da wata Farfesa Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito kotun majistare da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a, ta tasa keyar Farfesa Zainab Duke Abiola tare da ma’aikatan gidanta bisa laifin cin zarafin ‘yan sanda, Insifekta Teju Moses da ke tare da ita.

Alfijr Labarai

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya yi Allah-wadai da cin zarafin ‘yar sanda da Hadi da wasu ma’aikatanta na cikin gida da suka hada da ‘yar aikin gidan, Rebecca Enechido, da wani namiji da ake zargi a halin yanzu.

Matar ta yi ikirarin cewa Duke, wata ‘yar fafutuka ne, ta kai mata mummunar hari tare da wasu ‘yan aikinta a ranar Talata, 20 ga Satumba, 2022, a gidanta da ke Garki, Abuja, saboda ita yar sanda ce, ta ki keta darajar sana’arta ta hanyar aikata rashin gaskiya a gidanta

Alfijr Labarai

Sai dai kuma a kotu a ranar Juma’a, an hana Duke-Abiola beli, kuma an dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 5 ga Oktoba, 2022.

Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin a tsare ta a gidan yarin Suleja har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *