Alfijr ta rawaito Kotun Majistare mai lamba 54 da ke unguwar Noman’s Land a jihar Kano ta yanke wa wata matshiya, Zainab Salisu Sheka hukuncin watanni shida a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona.
Alfijr Labarai
Tun da fari, ƴan sanda ne su ka gurfanar da Zainab a gaban kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Mansur, bisa amfani da kayan ƴan sanda ta na bada hannu a danjar kan titin New Road da ke Sabongari.
Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Aminu Kawu ya roki kotu da ta karanto wa wacce ake tuhuma laifukan ta. Sai jami’in kotu Muhammad Zakirai ya karanto mata kuma ta amsa laifinta.
A nata bangaren mai laifin ta shaida wa kotun cewa aikin ne ya ke bata sha’awa shi ya sa ta yi.
Alfijr Labarai
Mai Shari’a a nasa bangaren da ya ke yanke hukuncin, alkali Mansur ya yanke mata watanni shida a gidan yari ko tarar Naira dubu 50.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller