Gwamnatin Zamfara Ta Sanar Da Sake Kulle Kananan Hukumomi 3 A Jihar

Alfijr ta rawaito gwamnatin Zamfara ta sanar da cewa za ta kulle kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi, biyo bayan barkewar hare-haren ‘yan bindiga a kan al’umma a ranar Juma a.

Alfijr Labarai

Matakin na kunshe ne a cikin sanarwa da kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara ya fitar a Gusau.

“Gwamnati ta ba da sanarwar dakatar da wasu manyan garuruwa tara domin dakile yawaitar hare-haren da ake kai wa a yankunan da lamarin ya shafa.

“Garuruwan Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da Mada.

“Gwamnati ta kuma sanar da rufe kasuwannin Danjibga da Bagega da kuma Colony zuwa Lambar Boko Road, Bakura zuwa Lambar Damri da Mayanchi- Daki Takwas zuwa Gummi Road.

Alfijr Labarai

“Sauran su ne hanyar Daki Takwas zuwa Zuru, Kucheri-Bawaganga – Titin Wanke, Magami zuwa Titin Dangulbi da Gusau zuwa Titin Magami.

Ya bayyana cewar an dauki matakan ne domin saukaka kokarin jami’an tsaro wajen fatattakar masu aikata laifuka a yankunan,” in ji gwamnatin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *