Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin lashe wata dattijuwa mai shekara 67, kan zargin ta da maita.
Alfijir labarai ta rawaito Kotun ya yanke musu hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan samun su da laifin kiran dattijuwar mai suna Ɗahare Abubakar, mayya sannan suka daɓa mata wuka har lahira.
Mai Shari’a Usman Maido, ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifin wadanda aka gurfanar.
Waɗanda ya yankewa hukuncin kisan su ne Da’luta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu da Ayuba Abdulrahman.
Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano
Tun da farko, mai gabatar da kara, LamiÉ—o Abba-Soron É—inki, ya shaida wa kotun cewa da misalin karfe 8.30 na safiyar ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 2023 ne waÉ—anda ake tuhumar suka hada baki wajen yin aika-aikan.
Ya ce bayan waÉ—anda ake tuhumar sun zargi Marigayiya ÆŠahare da maita ne suka bi ta gona É—auke da makamai, suka yi mata kisan gilla,
Ya ce an garzaya da ita zuwa Babban Asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar cewa ran dattijuwar ya yi halinsa.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Daɗin Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Wudil.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ