Wata Kotu Ta Daure Wani Basarake Ɗaurin Shekaru Goma Sha Biyar 15 A Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito wata babbar kotu da ke Ikeja ta yanke wa mai rike da sarautar Baale da ke Shangisha a unguwar Magodo a Jihar Lagos mai suna Mutiu Ogundare ɗaurin shekaru 15 bisa laifin yin ƙarya cewa an yi garkuwa da shi.

Alfijr Labarai

Alkalin kotun mai Shari’a Hakeem Oshodi ya yanke wa Ogundare hukuncin bayan ya kama shi da laifuka biyu da su ka haɗa da tayar da hankalin al’umma da kuma ƙaryar an yi garkuwa da shi.

Da yake jaddada hukuncin shi ma kaninsa, Opeyemi Mohammed, an yanke masa adadin shekarun 15 dai dai da na dan uwansa Ogundare.

Sai dai kuma kotun ta wanke Ogundare, Abolanle bayan da tun a baya ta gano babu hannunta a ciki.

Tuni aka ija keyarsu domin girbar abinda suka shuka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *