Wata Kura Ta Ƙwace A Kano, Ƴan Karota Na Neman Mai Ita Ruwa A Jallo

Alfijr ta rawaito Hukumar KAROTA ta jihar Kano ta ce tana ci gaba da neman wani mai baburin a-daidaita-sahu ruwa a jallo bayan ya ɗauko wata kura da ta yi ƙoƙarin tserewa a tsakiyar kasuwa.

Alfijr Labarai

Hukumar ta ce jami’anta suna neman ɗan Adaidaita sahun saboda abin da ya yi ya saɓa wa doka, don kuwa bai kamata ya ɗauko dabbar daji a cikin babur ba.

Mai magana da yawun hukumar, Nabulisi Abubakar ya shaida wa BBC cewa kura ba tunkiya ko akuya ba ce, dabba ce mai hatsari da bai kamata a bar ta tana gararamba a cikin mutane ba.

“Muna ci gaba da neman ɗan a-daidaita-sahun a yanzu haka, kuma muna da lambobin babura guda biyu da muke zargi, matuƙar kuma muka kama direban, to kotu za mu kai shi kai tsaye.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a kasuwar ‘yan canji ta Wapa da ke tsakiyar birnin Kano, daidai lokacin da mutane ke gudanar da harkokin rayuwa da suka saba.

Alfijr Labarai

Kurar dai wadda aka ɗauko a cikin ɗan sahu ta yi yunƙurin ƙwacewa ne lokacin da ta kufce daga hannun mai ita wanda fasinja ne, a tsakiyar kasuwar ta Wapa.

Hakan dai ya yi matuƙar ta da hankulan mutanen da suka fara gudu a tsakiyar kasuwa a daidai lokacin kurar ta fara kaiwa da komowa

Shugaban kasuwar ‘yan canji, Hussaini Abdullahi ya ce kurar ta ƙwace ne jim kaɗan bayan sun gama sallar la’asar, lokacin da baburin adaidaita-sahun da ya ɗauko kurar yaker wucewa.

A cewarsa, takunkumin da aka sanya wa kurar ya cire abin da ya sa mutane suka ƙara tsurewa ke nan.

“Duk da haka wasu masu taurin kai sun tsaya suna kallon abin da ke faruwa, yayin da wasu suka sheƙa da gudu. Allah dai ya kiyaye kurar ba ta fara bin mutane da gudu ba”.

Alfijr Labarai

Daga bisani ne mai kurar ya yi nasarar sake kama ta har ma ya mayar da takunkumin bakinta, kafin ya ɗauke ta su ci gaba da tafiya.

Hussaini Abdullahi ya ce: “a lokacin ba su san hukuma na neman mai a-daidaita-sahun ba, don kuwa ya zo ne kawai ya wuce ta Kasuwar

KAROTA sun ce da zarar sun kama a-daidaita-sahun da ya ɗauko kurar za su kai shi kotu

“Muna jin labarin cewa kura ta ƙwace, sai muka tashi jami’anmu waɗanda ƙwararru ne wajen tu’ammali da namun daji su je su kamo ta, amma suka yi rashin sa’a.”

Ya ce abin da irin waɗannan mutane masu yawo da namun daji ke yi, ya saɓa wa doka saboda yin hakan fataucin dabbobin daji kuma doka ta tanadi hukunci kan masu aikata irin wannan laifi.

BBC Hausa

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *