Alfijr ta rawaito wata mata ƴar kasuwa mai suna Monica Gambo, ta maka mijinta, Yakubu Gambo a gaban wata kotu da ke Nyanya Abuja, saboda ya hana ta haƙƙoƙinta na aure a yau juma a.
Alfijr Labarai
Monica ta shaidawa ai mai sharia a cikin kunshin korafin da ta a gaban kotu
“Mijina mazinaci ne, sai ya riƙa kawo yan matansa gida na ya na zina da su ko kunya babu.
Ni kuma ya hana ni duk wasu haƙƙoƙi na na aure, sabo da haka ni ba zan iya ci gaba da zama da shi ba,” in ji ta.
Ta kuma shaida wa kotun cewa mijin nata ya sha yi mata barazanar kashe ta tare da ƙwace mata dukiyatarta.
Bisa wadannan Dalilan na ke rokon kotu mai adalci da ta raba auren namu, sannan kuma kotu ta umarce shi da ya bar mata gidanta.
Alfijr Labarai
A nasa bangaren mijin da ake kara, Yakubu Gambo, mai gudanar da sana’ar ɗinki, bayan jin duk wadannan bayanan da mai sharia ya bashi dama, sai ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Shitta Mohammed, ya ɗage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 20 ga watan Satumba, na wannan watan
Ina son mu
Muma haka