Alfijr ta rawaito gwamnatin jihar Kano ta amince da biyan Naira miliyan 304 na alawus-alawus ga ma’aikata 287 na ɓangaren koyarwa na jami’ar Yusuf Maitama Sule, da suka cancanta.
Alfijr Labarai
kwamishinan yada labarai na jihar, Mal Muhammad Garba me ya fitar da wannan sanarwar a Kano a yau Juma’a.
Ya kara da cewa hakan ta biyo bayan taron majalisar zartarwa na jihar na mako-mako da aka gabatar
Kwamishinan ya ƙara da cewa za a rika biyan kudaden alawus-alawus ɗin ma’aikatan ne daki-daki a kowane wata daga watan Oktoba.
“Za a biya Naira miliyan 297 ga ma’aikatan fannin koyarwa da aka tantance, yayin da aka kiyasta Naira miliyan 6.5 don a biya sauran ma’aikata ilimi 10 da a ka cire sunayensu bisa kuskure a biyan kuɗin da ya gabata.
Alfijr Labarai
Majalisar ta kuma amince da fitar da Naira miliyan 82.1 ga jami ar Maitama Sule domin samar da ayyukan gyaran makaranta kai tsaye da kuma samar da kayan aiki a tsangayar kimiyya,” inji shi.
Haka kuma an amince da Naira miliyan 84.9 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jiha da ke Wudil, don biyan ɗalibai ne da su ka je shirin sanin makamar aiki a masana’antu, SIWES, da kuma alawus-alawus na zuwa makamar aiki koyarwa na zango biyu na 2019/2020 da 2021/2022 ga ma’aikatan ilimi da suka cancanta.