Wata Sabuwa! Yan Ta’adda Sun Sace Mahaifiyar ‘Yar Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A APC, AA Zaura

Alfijir

Alfijr ta rawaito wasu barayi da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, A.A Zaura, wato Hajiya Laure.

An sace mahaifiyar dan siyasar ne da asubahin yau Litinin kafin kiran Sallah, kamar yadda shugaban karamar hukumar Ungoggo, Abdullahi Garba Ramat, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Alfijr

Ramat yace an sace Hajiya Laure ne a gidanta dake garin Zaura a mazabar Rangaza ta karamar hukumar Ungoggo, kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar masa.

Sauran bayanai nanan tafe…

Slide Up
x