Kamfanin MTN Ya Sami Amincewar Bude Banki A Nijeriya.

Alfijr ta rawaito Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya sami sahalewar hukumomin Najeriya domin ya bude banki, kamar yadda kamfanin ya sanar ranar Litinin.

Kamfanin ya ce Babban bankin Najeriya ne zai sanar da ranar da aka amince mu fara aiki, kamar yadda doka ta samar.

Kamar yadda kamfanin ya sanar, sunan sabon bankin nasa MoMo Payment Service Bank Limited.

Alfijr

A watan Nuwamba aka ba MTN Nigeria tare da Airtel Africa amincewa ta wucin gadi domin su bude bankuna, inda suke sa ran jawo hakulan ‘yan Najeriya kimanin miliyan 38 da ba su da asusun ajiyar banki a kasar.

Kamfanin sai da ya jira amincewar na tsawon shekara biyu kafin aka amince ma sa ta hanyar ba shi lasisi.

Kamar yadda BBC Hausa ta wallafa

Slide Up
x