Yadda Hukumar Hisba Ta Kama Barayin Wayoyi A Masallacin Alfurkan Kano

Alfijr ta rawaito hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mutum takwas 8 maza da mata da take zargi da satar wayoyi da sauran manyan laifuka a masallacin Al-Furqan da ke Kano.

Harun Ibn Sina babban kwamandan hukumar na Kano ne ya tabbatar da kama matasan ga ’yan jaridu ranar Talata

Yace an kama su ne da yamma yayin da suke shan kwaya da sauran kayan maye a kusa da masallacin.

Alfijr

Ibn Sina ya alakanta wannan halayyar ta matasan a matsayin wacce ta sabawa addinin Musulunci, musamman a watan Ramadan.

Yayi kira ga al’umma da su sa ido tare da kai rahoton duk wani wanda suka gami suke kuma zargi da aikata ba daidai ba ga hukumar Hisba ko Jami an tsaro mafi kusa.

Alfijr

Ibn Sina ya ce za su mika wadanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki akansu

A karshe yayi kira ga Al umma dasu cigaba da basu hadin kai domin ciyar da Kano gaba.

Slide Up
x