Wata Sabuwa! Cacar Baki Ta Sake Kaurewa Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Bishop Kukah

Alfijr

Ba za mu taba ci gaba da gudanar da harkokin addini cikin tashin hankali ba, dole mu budo hanyar warware matsalolin da muke ciki a Nijeriya, saboda ‘yan kasa su sami ‘yanci da walwala.

Alfijr ta rawaito, cacar baki ta sake kaurewa a tsakanin Gwamnatin Tarayya da Bishop Mathew Hassan Kukah kan yadda al’amuran kasa ke gudana, inda ya kalubalanci ministan yada labarai, Lai Mohammed da masu taimaka wa shugaban kasa ta fannin yada labarai wato Femi Adesina da Garba Shehu da su shirya muhawara ta musamman kan nasarori da jam’iyyar APC da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari suka samu, tun daga lokacin da suka hau karagar mulki na tsawon shekaru bakwai.

Kukah ya ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kan martanin da mai magana da yawun shugaban kasa ya yi masa na cewa, “Kalamun Kakah sun kasance annoba, a baya ina daukansa mutumin kirki, amma a yanzu yana mummunar suka ga shugaban kasar Nijeriya.


A cewar malamin kiristan, ‘yan Nijeriya sun san gaskiya, yana mai ba da misali da ce ko matar shugaban kasa, Aisha Buhari ba ta goyon bayan dukkan manufofin mijinta.

Alfijr

Bishop Matthew Hassan Kukah ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta haddasa rarrabuwar kawuna a kasar nan bisa kabilanci da addini da bangaranci wanda hakan bai taba faruwa ba a tarihin Nijeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi da ta gabata a cikin sakonsa na bikin Ista.


Ya kara da cewa shugaba Buhari ya tarwatsa Nijeriya wanda babu wani abin da ya rage a kasar sai cin hanci da rashawa.

Alfijr


A cewar Kukah, babban kalubale da Nijeriya take fuskanta ba wai zaben 2023 kadai ba har da yadda za a samu hadin kan ‘yan Nijeriya.

Ya ce babbar matsalar da ke tunkarar kasar nan shi ne, hanyar da za a bi wajen sake gina kasar nan, idan har an samu gudanar da zaben 2023 lami lafiya.

Ya ce akwai bukatar kiristoci da musulmai su hada kansu wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu domin ceto kasar nan.

Alfijr


Kukah ya ce, “Akwai bukatar mu fara tunanin yadda Nijeriya za ta kubuta daga hannun ‘yan bindiga da masu garkuwa da sauran rikice-rikicen al’umma a kasar nan.

“Ba za mu taba ci gaba da gudanar da harkokin addini cikin tashin hankali ba, dole mu budo hanyar warware matsalolin da muke ciki a Nijeriya, saboda ‘yan kasa su sami ‘yanci da walwala.

Alfijr


“A shirye muke mu yi aiki tukuru wajen ganin mun magance matsalolin da suke damun kasar nan,” in ji Kukah.


A nata martanin fadar shugaban kasa ta mayar wa Bishop Mathew Hassan Kukah zazzafan martani kan hudubar da ya gudanar a ranar Lahadi lokacin bikin Ista, inda ta bayyana masa cewa ya cire rigar addini ya sa ka ta siyasa a fafata da shi.

Alfijr

Mai Magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana hakan a daren Litinin da ta gabata, inda ya bayyana cewa Kukah ya dade yana sukar gwamnatin shugaban kasa Buhari a wurin hudubarsa da yake yi a coci.


Ya ce maimakon Kukah ya tunatar da kiristoci muhimmancin bikin Ista, amma ya fake da sukar gwamnati na tsawon shekaru duk da kokarin da take yi, wanda ya nuna cewa yana siyasa ce kawai a fakaice.

Alfijr


Ya kara da cewa Kukah ya yi watsi da karantarwar Baibul domin, “Idan mutum yana tunanin cewa shi mai addini ne, to ya kiyaye harshensa kar zuciyarsa ta rude shi, wannan mutum zai kasance mai cikken addini.”


Mai Magana da yawun shugaban kasan ya ce ya kamata bikin Ista ya kasance lokacin yin fata nagari ga masu rike da madafun iko, domin a samu ci gaba mai dorewa.

Alfijr

Ya ce, “Wannan ba lokacin da shugabannin addini za su dunga shiga lamari na harkokin siyasa ba ne ko kuma yin siyasa da sunan addini, lokaci ne na hadin kai da samun fahimtar juna a tsakanin al’umma.


“Kukah yana amfani da mumbarinsa ta hanyar da ba ta dace ba wajen kawo rarrabuwar kai da karya dokar kasa, kuma a ko da yaushe kalamunsa na sukar gwamnati ne.

Alfijr

“Ya kamata shugabannin addini su sani cewa suna da dimbin mabiya da suke cikin gwamnati, su dunga musu adalci a kan abubuwan da suke gudanarwa.


“Da dadewa ‘yan Nijeriya sun san cewa Kukah ya dade yana sukar gwamnati, kuma a kullum sai ya bayyana yadda ya tsani wannan gwamnati. Idan ma yana bayyana ra’ayinsa ne na siyasa, to bai kamata ya dunga fakewa da rigar addini ba, domin hakan cin zarafin addini ne kai tsaye.

Alfijr

Garba Shehu ya kara da cewa, muna kira ga Kukah ya kyale gwamnati da wadanda suka zabe ta da ‘yan siyasa, shi kuma ya himmatu wajen gudanar da harkokin addini na, idan kuma bai ji wannan kiran ba, to ya ajiye rigar addini ya shiga siyasa domin ya gwada kwanjinsa,” in ji shi.

A wani martanin kuma, Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai bari wani ya karya dokokin Nijeriya ba, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya su barranta da mutane masu karya dokokin kasar nan, inda ya tabbatar da cewa ba zai taba lamuntar wani mutum ko kungiya ya tarwatsa Nijeriya ba.

Alfijr

Ya bayyana hakan ne ta bakin mai taimaka masa ta fannin yada labarai, Femi Adesina, jim kadan bayan kammala bude-baki da gwamnoni da ministoci da kuma shugabannin ma’aikatun gwamnatin tarayya

Kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa

Slide Up
x