Yadda Jami an Tsaro Sukayi Yinkurin Kame Barr Muhuyi Rimin Gado

Alfijr

Alfijr ta rawaito yunkurin da ‘yan sanda suka yi na kame tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, inda suka yi Kawanya a gidan Muhuyi Magaji da yiwuwar kama shi da aka yi a daren Lahadin da ta gabata ya samu cikas

A daidai lokacin ne babban dan gidan Barista Muhyi Magaji, Zahraddin ya hango wasu motoci da ake zargin suna kusa da gidan da ke Unguwar Sharada daura da titin Yahaya Gusau a cikin birnin Kano.

Da dan Muhuyin ya fara hango wasu motoci ne daga nesa yayin da wani mutum a kan babur ya zo kusa da gidan da daddare inda ya tambaye su cewa saboda kalubalen tsaro, me ke faruwa, sannan me kuke yi a nan, sai suka shaida wa babban dan Muhuyi cewa ‘yan sanda ne da ke sintiri.

Alfijr

Sannan kuma daya daga cikinsu ya nuna wa masa ID card dinsa, daya kuma a kan babur ya nuna masa ID card dinsa amma constabulary, sai Zahraddin ya koma gida ya sanar da Barista Muhyi abinda ke faruwa a waje.

Sannan yaje ya dauko motar Barista Muhyi Magaji ya fito da ita ya fara tafiya, daga cikin motocin dake jira daga nesa ta bi motar sannan Zahraddin ya zagaya mahadar Gadon kaya, wani gareji yaje ya ajiye motan ya koma gidansu a lokacin Barrister Muhyi ya samu hanyar ficewa daga gidan.

Alfijr

Daga baya ya je sashin ‘yan sanda na Sharada ya kai rahoton lamarin inda suka ce ba su da masaniyar wani samame da ‘yan sandan suka yi.

Lokacin da Zahraddin Muhyi ya koma gida sai ya hangi motar da ke tsaye ta sake dawowa tare da lura da cewa Jami an tsarin ba su bar unguwar ba sai da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.

Alfijr

Zahraddin Muhyi Magaji ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan yankin Sharada ta ba shi hadin kai sosai a lokacin da take karbar bayanin abin da ya faru a kusa da gidan nasu da daren Lahadi.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto Muhuyi Magaji Rimin Gado baya gidan sa inda yunkurin kamashi bai yi nasara ba .

Alfijr

Tun bayan dakatar da shi a ranar 5 ga Yuli, 2021 da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi bisa shawarar majalisar dokokin jihar Kano tsohon shugaban yana takun-saka da gwamnatin Ganduje.

Kokarin samun Barrister Muhyi Magaji bai cimma ruwa ba saboda wayarsa a kashe.

Amma alfijr ta tattauna da wani daga cikin makota game da abinda ya faru, ya tabbatar da jin harbe harbe yayin sumame a daren lahadin