Alfijr ta rawaito Nasir Salisu Zango na cewa, labarin da ya motsa min Zuciya…
Yaro ne karami wanda a fuska ban yi zaton ya haura shekara 8 ba, amma mahaifin sa ya turo shi Kano almajiranci daga garin Gamawa a jihar Bauchi
Ba Zuwan sa almajirancin ne yafi damu na ba, domin wannan Ai an saba, amma na farko kankantar yaron nan abar dubawa ce gashi ilahirin jikin sa yayi kaca kaca da tabbai na dukan bulala,
Alfijr
Gaskiyar magana wanda yayi masa wannan dukan bashi da tausayi kuma bai cancanci ya amsa sunan Malam ba.
A jawabin da yake bani,yaron ya ce Malamin sa ne yake dukan sa saboda idan yaje bara baya kawo masa komai,wai ashe idan an fita bara sadakar farko ta Malam ce.
Alfijr
Yaron yaci gaba da cewar mahaifiyarsa ta rasu kuma mahaifinsa ne ya kawo shi almajiranci, kuma yace bai San unguwar da makarantar tasu take ba, kwana biyu kenan ya fito bara yayi batan kai ya kasa gane makarantar tasu.
Dan Uwan mai unguwar kofar mata mai suna Hussaini shine ya karbi yaron daga hannun wadanda suka tsinto shi.
Yanzu haka dai mun hada su da Sani Bundin wani matashi jajirtacce dake tsayawa marasa gata, na kuma hada su da hukumar yaki da Bara ta jihar Kano karkashin Sheikh Muhammad Al Bakri mikha’el domin a dauki mataki na Gaba.
Alfijr
Babban abin takaici ne ace har yanzu a Kano ana karbar irin wadannan mini minin yaran da sunan an kawo su bara gaskiya bai dace ba.
Yanzu wannan yaron dai ba a nuna masa jin kai ba, bai samu shakuwa da iyaye ko yan Uwa ba, idan ya girma a titi wa kuke tunanin zai tausayawa?
Alfijr
Barin irin wadannan yara da muke gani suna gararamba a titi babbar masifa ce, wacce idan ta tunkaro bazata takaita akan wanda ya jawo ta kadai ba,ya kamata mu ribanya kokari wajen yaki da wannan annoba.
Zamanin da, da na yanzu ba daya bane.
Ina goyon bayan karatun alkur’ani kuma ina goyon bayan hana bautar da kananan yara
Allah ya kawo mana karshen matsalolin dake damun Mu.
Alfijr
Kamar yadda Nasir Zango ya wallafa kenan.