Yadda Ta Kasance Da Ɗan China Da Ya kashe Ummita A Kotu Yau

Alfijr ta rawaito kotun majistare mai lamba 30 da ke zaman ta a titin Zangeru da unguwar sabon gari a jihar Kano ta Aike da dan kasar China mai suna Frank Geng Quanrong, mai shekaru 47 zuwa gidan yari bisa laifin kashe budurwarsa

Alfijr Labarai

Kunshin tuhumar dai shine, Ana zargin Quanrong da laifin kashe tsohuwar budurwar sa, Ummukulthum Buhari mai lakanin Ummita

Rahotanni sun bayyana cewa Quanrong ya bi marigayiya Ummukulthum har gidan iyayenta ya kutsa cikin dakinta sannan ya riƙa daɓa mata wuka a yammacin ranar Juma’a.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari a Hanif Sanusi Yusuf, da yake yanke hukuncin, ya tuhumi Quanrong da laifin kisan kai, wanda ya ci karo da sashe na 221 na dokar hukunta manyan laifuka.

Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, wata mai kamawa

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *