Alfijr ta rawaito Kotun Ma’aikata da ke zamanta a babban birnin Abuja ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta janye yajin aikin da take yi.
Alfijr Labarai
Alkalin kotun da yake gabatar da hukunci kan bukatar da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar.
Shari at ta biyo bayan da gwamnatin tarayya ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe watanni bakwai tana daka shi.
Polycap Hamman, alkali ne da ke sauraron shari’ar sakamakon hutun da sauran kotuna suke, kuma ya mayar da karar zuwa ga shugaban kotun ma’aikata don ya sake bai wa wani alkali shari’ar.
Alfijr Labarai
Shugabannin kwadago na kasar sun ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan da tattaunawarsu da kungiyar malaman jami’o’in wato ASUU ta gaza haifar da da mai ido
Babban burin Gwamnatin tarayya na garzayawa kotun shine, tana son kotun ta bayyana halarci ko haramcin yajin aikin ASUU.