Ƴan China Sun Kirƙiro Takunkumin Fuska Mai Gano Cutar Korona A Cikin Minti 10

Alfijr ta rawaito wasu gungun masana kimiya na kasar China sun ƙirƙiro wani takunkumin fuska, wanda zai iya gano mai ɗauke da ƙwayoyin cutar korona cikin mintuna 10 da haɗuwa da mai sanye da takunkumin.

Alfijr Labarai

Kwayoyin cutar korona, wacce aka fi sani da COVID-19, na fito wa ne daga jikin mai ɗauke da su ta hanyar magana, tari ko attishawa, ko dai wata mu amula.

Takunkumin mai ɗauke da na’ura, wanda masu binciken daga Jami’ar Tongjin suka ƙirƙira, ka iya gano ƙwayoyin cuta ta numfashi na yau da kullun, gami da mura da coronavirus, a cikin iska a cikin ɗigon ruwa ko iska, sannan ya sanar da nasu sanye da shi a fuska ta wayoyin su na salula.

Dangane da binciken da aka buga a cikin mujallar, takunkumin mai ƙarfin ɗaukar yanayi, yana iya auna samfuran ruwa masu girman 0.3 na microliters da samfuran iska a ƙarancin girman 0.1 femtograms a kowace millilita.

Alfijr Labarai

Fang Yin, farfesa a Tongji ya ce ma’aunin gano ruwa mai ɗauke da sunadaran ƙwayoyin cuta a cikin ɗakin da ke kewaye ya kasance “kusan sau 70 zuwa 560 ƙasa da adadin ruwan da ake samarwa a hanci, tari ko magana.

Daily Nigerian

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *