
Alfijr ta rawaito ta ruwaito cewa, hukumar zabe ta ayyana Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Doguwa/Tudunwada a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai a baya ya bayyana cewa Doguwa na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 39,732 inda ya doke abokin hamayyarsa Yushau Salisu Abdullahi na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) wanda ya samu kuri’u 34,798.

Amma a cikin sabbin zababbun mambobin da aka fitar, sunan Doguwa bai fito fili ba.
A zaman da hukumar ta INEC ta yi, ta bayyana cewa an tursasa ta.

Kamfanin dillancin labarai na News Point Nigeria ya bayar da rahoton cewa, biyo bayan rikicin zabe da aka samu a mazabar bayan kammala zaben, ‘yan sanda sun cafke Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane da kuma kona sakatariyar jam’iyyar NNPP, zargin da dan majalisar ya musanta da kakkausar murya.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa akalla mutane uku ne suka mutu yayin da aka kona sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada tare da kona mutane biyu har lahira.
Daga nan ne aka gurfanar da Doguwa a gaban kotun majistare kan zargin kisan kai, kone-kone da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, daga bisani aka tsare shi a gidan yari.

Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin din da ta gabata ta amince da belin dan majalisar kan kudi naira miliyan 500, amma ta hana shi shiga mazabarsa a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da ke tafe.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai