Alfijr ta rawaito, hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Binuwai, Dokta Emmanuel Shior, ne ya bayyana hakan a Makurdi ranar Laraba a wajen rabon kayan agaji na wata-wata ga ‘yan gudun hijira.
Alfijr Labarai
Ya lissafa sassan babban birnin Benue da abin ya shafa kamar Titin Naka, Achusa Kucha Utebe, Gyado Villa, Judge’s Quarters Extension da sassan Nyiman da dai sauransu.
Shior ya lura cewa ambaliyar ba ta kasance mai muni ba a jihar a baya.
Ya ba da tabbacin cewa kwamitin da ke kula da ambaliyar ruwa na jihar ya amince da fadada wasu sansanonin da aka zabo a Makurdi, Guma da Logo domin daukar wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Ya kara da cewa hare-haren baya-bayan nan da aka kai wa wasu al’umomi a jihar ya yi sanadiyar raba mutane sama da 400,000 da matsugunansu.
Ya ce gwamnatin jihar na bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa da kuma ‘yan gudun hijira daga Kamaru da ke zaune a karamar hukumar Kwande da ke jihar.
Alfijr Labarai
Ya kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta taimaka saboda nauyin da ke wuyan gwamnatin jihar ke yi.
Shior ya ce maharan sun kashe da raunata tare da lalata kayayyakin more rayuwa kamar kasuwanni, coci-coci, da makarantu a cikin al’ummomin da aka kai hari.
(NAN)