Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Zargin Siyar Da Gine-Ginen Kotu

Alfijr ta rawaito kwamishinan shari’a, Musa Abdullahi Lawan ya ce babu wani shiri da gwamnatin Kano ta yi na sayar da wasu kotunan shari’a a jihar.

Alfijr Labarai

Abaya dai an ji yo wasu Lauyoyin da ke Kano sun garzaya wata babbar kotun Kano, suna neman ta hana gwamnatin jihar ɗaukar wani mataki a kan gine-gine da harabar kotunan.

Kotunan da ake zargin siyarwar dai sun haɗa da Babbar Kotun Shari’a ta Gidan Maitasine, Ƴan Awaki, Kotun Shari’a ta Ƴan Alluna, Kotun Shari’a ta Shahuci, da Kotun Shari’a ta Goron Dutse, da Babbar Kotun Shari’a ta Kasuwar Kurmi, da Kotun Shari’a ta Filin Hockey.

Da yake mayar da martani, Lawan, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Ayyuka kan Sauya-fasali da Ci gaban Kaddarori na Jihar Kano, ya ce ikirarin da lauyoyin su ka yi karya ce, maras tushe da siyasa da kuma ƙin gaskiya.

Alfijr Labarai

Abdullahi ya ce: “Gwamnatin jihar ba ta da shirin sauya wa Kotun Shari’a ta Goron Dutse da Kotun Shari’a Filin Hockey, Hausawa waje ba

“Hukuncin da gwamnatin jihar ta yanke na mayar da Kotun Shari’a ta Ƴan Awaki ya faru ne saboda tashar motar Kofar Wambai ta matso har jikin ginin kotun.

“Don haka bai kamata a zauna a kotun ba idan akwai hayaniya gami da karar motoci ko wani abu da zai ɗauke hankalin alkali da jami’an kotu da kuma masu ƙara.

“Kotu tana bukatar yanayi na natsuwa don gujewa tabarbarewar shari’a.

Alfijr Labarai

“An mayar da Kotun ƴan Awaki ta koma titin Sabuwar BUK, inda ta kasance sashen kotunan shari’a gaba ɗaya da suka haɗa da, kotun shari’a, babbar kotun shari’a ta da kotun ɗaukaka karar shari’a da za a kammala a karshen watan Satumba. 2022, “in ji shi.

Lawan ya ce sauran kotunan Shari’ar na Kasuwar Kurmi da Ƴan alluna duk sun yi cikin kasuwa da yawa kuma ana samun hayaniya yayin yin Shari’a.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *