An Gano Mushen Dabbobi Da Ake Siyarwa Mutane A Abbatuwa Kano

Alfijr ta rawaito Jami’in Hukumar kula da kare hakkin mai siya da mai Siyarwa (KSCPC) ta Jihar Kano, ta ce ta gano tare da kama wasu matattun dabbobi a Unguwa Uku Yan Awaki Abbatoir da ke karamar hukumar Tarauni a jihar.

Alfijr Labarai

Mukaddashin Manajin Darakta na hukumar, Baffa Babba-Dan’agundi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Musbahu Yakasai ya fitar a Kano ranar Litinin.

Babba-Dan’agundi, wanda babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin tabbatar da ingancin kayayyakin masarufi, Alhaji Salisu Muhammad ya wakilta, ya ce majalisar ta samu labarin dabbobin da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Litinin.

Mun samu labari daga wasu nagartattun mutane cewa an kawo wasu dabbobi da suka hada da rago da akuya bayan an yanka su a wani wuri.

Alfijr Labarai

Sakamakon haka suka fara zargin cewa sun riga sun mutu kafin a yanka su.

Nan take tawagarmu ta dauki mataki tare da kame dabbobin a kokarin da muke na kare mutanen Kano daga amfani da kayayyakin da ba su da kyau, na jabu lalatattu.

Ya yi nuni da cewa majalisar ta gayyaci wani Likitan Dabbobi domin ya gwada dabbobin ko sun dace da cin naman, tare da tabbatar da ko da gaske yawancinsu sun mutu kafin a yanka su.

Alfijr Labarai

Babba-Dan’agundi ya yi kira ga mahauta a Unguwa Uku ‘Yan Awaki da sauran na jihar Kano baki daya, musamman masu yin damfara da su daina irin wannan aika aika ko kuma su fuskanci fushin doka

.(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *