
Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce kimanin jami’an tsaro dubu 18,748 ne aka baza a fadin jihar domin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 18 ga watan Maris.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labara na Ƙasa a Talata a Kano.

Ya ce ƴan sandan da sauran jami’an tsaro za su samar da cikakken tsaro a runfunan zabe dubu 11,222 da ke mazabu 484 da ke fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Dauda ya ce tuni aka bayar da umarnin gudanar da aikin tsaro ingantacce ga kwamandojin yankin da jami’an ƴan sanda na Caji-ofis domin aiwatarwa.

Ya kuma tabbatar da cewa ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun shirya tsaf don kare masu kada kuri’a da jami’an INEC a lokacin zabe da kuma bayan zabe.
“Ina ba da tabbacin tsaro kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda cewa za su yi zaɓe cikin yanci a ranar 18 ga Maris ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ
Alhamdulillah, Ma Sha Allah
My name is Doctor Kabir Excellent pharmacy I need government to give peace and unity in Kano what Allah be recorded no body can be rejected