Baku Da Hujjar Cewa Ƴan Nijeriya Na Fama Da Yunwa A Ƙasar! In ji Buhari

Alfijr ta rawaito Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya kalubalanci ‘yan kasar cewa ba su da wata hujja da za su ce yunwa ta takura musu, ganin yadda Allah ya baiwa Nigeria kasar, kasar noma.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a wata hira da gidan Talabijin na TTV, tare da Halilu Getso fitattaccen ɗan Jarida a Nijeriya.

Faɗin ya zo ne kan tambayar da ake wa Buharin cewa ana fama da yunwa a kasar.

Sai Buhari ya ce duk wanda ya ce yana jin yunwa to ya dauki kayan aiki ya nufi gona.

Ya ce rufe kan iyakoki da gwamnatin sa ta bullo da shi ya haifar da samar da isasshen abinci a cikin kasa.

Kuma shugaban ya bayyana cewar wata uku dai idan kudinka na halaline ya kamata ka canja su, idan kuma a wata uku sunyi kadan to ina tsammani akwai ha inci a cikin lamarinka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *