Alfijr ta rawaito an gurfanar da wani Magidanci a wata kotun majistare da ke zamanta a Ikeja mai shekaru 42, Austin Anthony, a ranar Talata bisa zarginsa da cin zarafin matarsa tare da raunata jaririnsa ɗan wata uku da haihuwa a hannu.
Alfijr Labarai
Kunshin tuhumar ya bayyana wanda ake karar, mai sana’ar gasa burodi, wanda ke zaune a gida mai lamba 16, layin Ajibade, Baruwa Ipaja a jihar Lagos, da laifin cin zarafin ƴar sa da illatata da kuma barazana ga rayuwar ta.
ASP Raji Akeem, ɗan sanda mai gabatar da kara, ya shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Satumba a gidan wanda ake kara.
Raji ya ce faɗa ne ya ɓarke tsakanin wanda ake kara da matarsa, Ifeyinwa, kan gazawar mutumin na daukar nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na miji da kuma uba ga ‘ya’yansu.
Ya kuma bayyana wanda ake tuhumar da karfi ya fizge jaririn nasu dan wata uku daga bayan mahaifiyarta kuma a cikin haka; jaririn ya samu rauni a hannunsa
Alfijr Labarai
Mai gabatar da kara ya kuma ce wanda ake karar ya lakaɗa wa mai ƙarar dukan tsiya tare da turo ta daga wani bene zuwa ƙasa.
“Hakan ya sa ta babballe a kafafunta kuma ta samu munanan raunuka a jikinta,” in ji shi.
Akeem ya kuma ce wanda ake tuhumar ya yi barazanar kashe matar ta sa da wukar kicin.
Laifukan, a cewar mai gabatar da kara, sun saɓa da sashe na 56, 172, 245 da 246 na dokokin laifuka na jihar Legas, na 2015.
A nasa bangaren wanda ake tuhuma ya musanta laifin da ake tuhumar sa da shi.
Alfijr Labarai
Alkalin kotun, B. O. Osunsanmi, ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Osunsanmi ta ɗage sauraron karar har zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller