Burina Samun Matar Da Zan Aura, Domin Dana Ya Gaji Dukiyata! In ji Bobrisky, Wanda Ya Mai da Kansa Siffar Mata

Alfijr ta rawaito Fitacciyar shahararriyar ɗan Daudu wato, Bobrisky ya gabatar da wani muhimmin roko game da abin da yake so a halin yanzu

Alfijr Labarai

Dan Daudun ya bayyana cewa yana neman mace mai haihuwa yayin da ya bayyana aniyarsa na samun zukekekiyar yarinyar da zai aura don samun magaji.

Bobrisky ya bayyana wasu kadarorin da ya mallaka da ‘Yar da zai haifa za ta gada, kuma ya bayyana cewa zai rubuta wasiyyarsa a ranar da ya samu yayi wuf da matar da zai aura.

Ya yi kiran ne a shafinsa na Instagram, in da ya ce ga duk wata kyakkyawar yarinya a Amurka ko Burtaniya da ke da sha’awar zama matar da zata haifa masa mai gadonsa, to a shirye yake.

Alfijr Labarai

Ya kuma ambaci wasu kadarorin da ya mallaka tare da bayyana cewa shekarun baya ina da kadarori da yawa, ina buk’atar yaron da zan barwa komai, babu wanda yasan lokacin da mutuwa zata zo.

Bibrisky ya kuma bayyana cewa zai bai wa mahaifiyarsa makudan kudade:

“Tun a shekarar da ta gabata na damu matuka game da samun magaji, ya kamata yarona na fari ya kasance mace, da zarar an sameta, zan rubuta wasiyyata domin ina kaunar ya mace.

Jama a da dama sun mayar masa da martani game da sakonni nasa, yayin da wasu ke san barka wasu ke Alawadai

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *