Dubun Wani Dan Damfara Mai Canjawa Mutane ATM A Wajen Cirar Kudi Ta Cika A Kano

Alfijr ta rawaito dubun matashi mai zamba a bakin ATM dake fadin jihar Kano ta cika

Alfijr Labarai

Wakilin Alfijr ya ci karo da wasu mutane suna ragargaza wannan matashin, matsawarsa ke da wuya sai ake bayyana masa abin da ke faruwa kamar haka.

Ya fara da cewa, wannan da kuke gani, sune masu zuwa ATM machine suna yiwa mutane wayo su chanja musu ATM din su, su kewaye zuwa wajen masu POS suyi withdrawing kudi.

Ganau din ya kara da cewa, sun zo wajen mu a Kundila, sun yi withdrawing 450,000 da dare, wayewar gari sai ga Jami an yan sanda daga daga CID sun zo an kama mu saboda wata Hajia tayi korafin an chanja mata ATM an Kuma kwashe mata 1.5 million.

Alfijr Labarai

Muna ta kokarin warware wannan matsalar da muka shiga sai Jiya da dare ya sake zuwa zai cire 150,000 da ATM na wani (Nasiru Hassan, access bank) dama mun gane shi nan aka kama shi, ba musu yace ga kudin mu 450,000 mu rufa masa asiri bai san za a zo bincike shagon mu ba da bazai zo yayi transaction a gurin mu ba.

Mun Kai shi Police station a daren, yau zaa tafi dashi CID.

Idan sun yi transaction a wajen ka to ka yi kokarin sanar da hukuma, domin sun cire 250,000 da 200,000 a Kasuwar Tarauni a wajen masu POS biyu kafin suka zo wajen mu suka cire 450,000.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *