Alfijr ta rawaito Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeria a ranar Alhamis ta amince da daukaka karar da ake tsare da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.
Alfijr Labarai
Kotun ta kuma sallame tare da wanke shugaban haramtacciyar kungiyar da aka kama.
Lauyan Kanu kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Ifeanyi Ejiofor, ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.
“An amince da daukaka kara, Oyendu Mazi Nnamdi KANU, an kuma sallame shi.
Mun yi nasara! ” ya rubuta. Kanu ya shigar da kara a ranar 29 ga Afrilu mai lamba CA/ABJ/CR/625/2022, inda ya nemi a sake shi kuma a wanke shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller